Covid-19: An Sake Saka Dokar Takaita Zirga-Zirga A Najeriya

Nigeria COVID-19

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake kakaba dokar takaita zirga-zirga, biyo bayan karuwar asarar rayuka da adadin masu kamuwa da cutar Covid-19 a wasu kasashe a fadin duniya, da kuma hatsarin da hakan ke haifarwa ga nahiyar Afirka.

Gwamnatin ta Najeriya dai ta sake waiwaiye ne kan matakan dakile Yaduwar cutar ta korona a kasar ta hanyar dawo da dokar hana fita daga karfe 12 dare zuwa karfe 4 na asuba a dukkan fadin kasar, wanda tuni ya fara aiki daga daren Litinin, 10 ga watan Mayu.

Kazalika gwamnatin ta haramta bude wuraren shakatawa na dare da motsa jiki har sai baba ta gani.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin gudanarwa na shugaban kasar dake yaki da cutar, ya amince da soma ba da allurar rigakafin Astrezeneca karo na biyu a fadin kasar

Baya ga haka, Shugabannin kasashe da na kungiyar ECOWAS sun kayyade kudin gwajin cutar COVID-19 a kan dala $50 a duk wuraren shiga kasashen yakin da zai fara aiki daga ranar 17 ga watan Mayu shekarar 2021.

A wani labarin kuma adadin mutane dubu 96,559 aka yiwa zagaye na farko na allurar rigakafin Covid-19 ba tare da wata tangarda ba a Abuja, babban birin tarayyar Najeriya ya zuwa yanzu.

Babban sakataren hukumar kula da lafiya a matakin farko na Abuja Dr. Ndaeyo Iwot, a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya kan allurar rigakafin Cutar COVID-19 a Abuja, ya bayyana cewa wannan adadin da aka samu, na daga cikin jimlar Mutane 248,400 da aka yiwa allurar ya zuwa yanzu a fadin kasar.

An soma zagaye na farko na aikin ba da rigakafin ne a kasar, a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2021.

A cewar Jami’ar gudanar da shirye-shirye a Hukumar Kula da rigakafi ta Abuja Salome Tor, an bayar da allurar rigakafin kyauta ne a dukkan Asibitocin gwamnati da kuma zababbun cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko, da kuma wasu wuraren da aka kebe na dan lokaci domin wannan aiki.

Ko da yake ta ce, da farko an yi ta samun shakku game da karbar allurar, amma jajircewa da ka yi wajen fadakar da jama'a ne ya taimaka aka samu wannan gagarumar nasara.

Ta kuma kara da cewa ana bayar da allurar ne ga wanda ya kai shekaru 18 zuwa sama.