Hukumomin Beijing sun sake daukar tsauraran matakan kulle jama’a da hana zirga-zirga tare da gudanar da gwajin cutar COVID-19 mai yawan gaske akan mazaunan birnin, bayan da aka sake samun barkewar cutar ta COVID-19 a daya daga cikin manyan kasuwannin saida kayan abinci na birnin.
Babban birnin kasar na China ya shiga cikin wani yanayi wanda kafafen yada labaran kasar suka bayyana a matsain tamkar "yanayin yaki" bayan da aka samu rahoton mutum 106 sun kamu da cutar a kusa da wata kasuwar saida kayan abinci ta Xinfadi da ke gundumar Fengtai a kudu maso yammacin Beijing.
Hukumomin birnin sun tura jami’an yaki da annoba 100,000, kuma sun sanya tsauraran matakan kulle a aƙalla yankuna 28, makarantu da wuraren wasanni da aka shirya budewa yanzu za su ci gaba da kasancewa a rufe.
Har ila yau jami'ai a Beijing suna hana mazauna birnin da ke zama a yankunan da ke tattare da matukar hadarin COVID-19 fita babban birnin, haka kuma an hana masu tasi da sauran motocin haya fita birnin da fasinja.
Masu sharhi sun ce, daukar tsauraran matakai na da mahimmanci ga jam'iyyar kwaminisancin China ta (CCP) bayan ta samar da kwarin gwiwa a cikin gida ta hanyar ayyana nasara kan yaki da COVID-19, duk da cewa da farko an yi rufa-rufa an kuma samu mishkila.
Amma duk da haka wasu kwararru sun yi imanin cewa, matakan da hukumomin Beijing suka dauka sun yi tsanani, kuma mazauna birnin suna yi kira da a dauki matakai masu sassauci a yaki da annobar.