Hukumomi a Kenya sun saka dokar hana fita a unguwar Eastleigh da ‘yan kasar Somalia keda tarin yawa a birnin Nairobi, saboda yawan kamuwa da coronavirus.
WASHINGTON DC —
Yayin da aka shiga mako na biyu na rufe anguwar Eastleigh ta ‘yan Somalia dake birnin Nairobi, harkokin kasuwanci na fuskantar kalubale.
Wani mai sayar da kayan bukatun jama’a Mohamed Said, ya ce kasuwanci ya lalace saboda mutane kalilan ne ke iya fitowa domin su sayi kaya.
Hukumomin Kenya sun rufe yankin ne zuwa 20 ga watan Mayu, bayan an tabbatar da mutane 29 sun kamu da coronavirus a wuni guda.
Hukumomin sun bada dama ne kawai ga masu sayar da muhimman kayayyakin bukatun jama’a, kamar masu sayar da magunguna da abinci su kadai ke iya shiga wurin.