Al’ummar musulmi a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da addu’o'i a jiya Talata don raya daren Lailatul Kadr, da neman falalar daren na 27 ga watan Ramadan.
Al’ummar musulmin kasar sun shafe daren jiya talata ana addu’oi a babban masallacin juma’a na birnin Yamai, inda dimbin musulmi suka hallara domin raya daren na Lailatul Kadar a hukunce.
A bana an karkatar da addu’oin wajen neman mafitar annobar coronavirus da ta addabi duniya baki daya. Ustaz Moha Hlalil jigo na kungiyar addinin islama ta AIN na daga cikin wadanda suka shugabancin zaman raya daren ya ce, yana kira a al’immar musulmin duniya su dage da addu’o’i kan wannan annoba ta coronavirus, sannan su ci gaba da bin matakan da hukumomin lafiya da gwamnatoci suka umarce su da shi.
Firaim minister Birgi Rafini ne ya jogroancin tawagar mambobin gwamnati a wurin wadanan addu’oi.
Ya ce, “muna fatan Allah ya albarkaci Nijer ya kuma albarkaci al’ummarta ya kuma yi mana tsari daga wannan muguwar cuta ta coronavirus kuma muna fatan Allah ya kara tsare al’ummar Nijer daga wannan bala’i domin mun yi amannar cewa ubangiji Allah ne ke tsare mu da sharrin wannan kwayar cuta. Anan ina sake kira ga al’umma a ci gaba da yin biyayya ga ka’idodin riga kafin da hukumomi da likitoci suka shimfida”.
Su ma mutanen gari da suka halarci zaman addu’oin sun bayyana fatansu. Daren Lailatul Kadr wanda malamai suka bayyana a matsayin daren da ya fi kowanne dare daraja a wajen musulmi kasancewar a cikinsa ne Allah ya saukar da alkur’ani mai tsarki, wani lokaci ne da al’ummar musulmi ke shafe dare a masallatai don yawaita addu’oi da ibada domin koyi da annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. abinda ya sa ranar 27 ga watan Ramadan ke matsayin ranar hutu a hukunce a ko ina a fadin kasar Nijar.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5