Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce, za’a fara sassauta dokokin coronavirus a mafi yawan yankunan kasar, duk ko da cewa wadanda suka kamu da cutar a kasar sun zarce 12,000.
A jawabinsa da aka yada ta kafar telebijin a yammacin jiya Laraba, Ramaphosa ya sanar cewa za su fara tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki akan tsara yadda ya zuwa karsahen watan Mayu, mafi akasarin kasar zai kasance a mataki na uku, inda za a bude wasu bangarori na kasuwanci.
Matakin Afirka ta Kudu na takaita yaduwar coronavirus ya ta’allaka ne akan tsarin matakai, inda matakai 5 suka kasance mafi tsauri.
Kasar ta shiga mataki na 4 a ranar daya ga watan Maris inda ta bai wa jama’a damar su fito waje don motsa jiki da kuma bude wasu sana’o’i.
Ramaphosa yace, wasu sassan kasar inda ake da yawan kamuwa da cutar za su ci gaba da kasancewa a mataki na 4, kana za a takaita tafiye-tafiye zuwa inda yankunan da sabin kamuwa suka yi kasa.