Addadin mutane da suka mutu a sakamakon annobar COVID-19 a fadin duniya ya zarce dubu dari uku da Hamsin.
Karin ya biyo ne bayan Koriya ta Kudu ta bayyana sabbin kamuwa da cutar mafi yawa a cikin kwanaki 49 a yau Laraba.
Hukumomi suna mai da hankali wajen gwajin ma’aikatan kamfanin sai da kayyaki ta yanar gizo na Coupang, bayan da aka alakanta mutane da dama da suka kamu da cutar a kamfanin dake wajen Seoul.
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ya Koriya ya Kudu, ta ce in banda hudu daga cikinsu, dukkan sababbin kamuwa da cutar daga yankin Seoul ne.
Kasar ta kasance daga wuraren farko da aka samu barkewar annobar coronavirus amma duk da haka, bata kasance daga cikin jerin kasashe 50 dake kan gaba da yawan wadanda suke fama da da cutar ba, bisa alkaluman da cibiyar John Hopkins dake Baltimore.