Jami’ai a kasar Philippines sun nuna damuwa matuka kan cewa za a samu bazuwar coronavirus mai muni a kasar, a daidai wannan lokaci da dubban mutane suke tsugune a wata cibiyar da ake tsugunar da mutanen da aka dauko daga tsibirin Luzon.
Mazauna tsibirin sun fita cikin dokar hana zirga zirga ala tilas, yayin da mahaukaciyar guguwar Typhoon Vongfong ta tasar ma tsibirin da ruwan sama kamar da bakin kwarya da iska mai karfi.
A Wuham na kasar China, inda cutar coronavirus ta faro a bara, jami’an kiwon lafiya sun fara gwajin gama gari bayan bayyanar wasu sababbin nau’ukan cuta masu kama da juna. Ana sa ran gwajin miliyoyin mutane zai dauki kiwanaki goma.
A yau Juma’a ne jirgin ruwan sojan Amurka na USNS Mercy dake dauke asibitin dakarun ruwa yake barin birnin Los Angeles. Jirgin ruwan ya isa tashar jiragen ruwan Los Angeles ne a ranar 27 ga watan Maris domin taimakawa asibitocin jihar California da suka batse yayin annobar coronavirus. Ma’aikatan lafiya 60 na cikin jirgin saura kuwa suna aiki a gidajen kula da tsofaffi.
Itama kasar Rasha ta shirya tsaf ta gudanar da gwajin gama gari a yau Juma’a. Rasha ita ce kasa ta biyu mai yawan mutanen da suka kamu da COVID-19 a duniya, inda sama da mutum dubu 250 ke dauke da cutar. Amurka dai ita ce ta farko a duniya da mutum miliyan daya da dubu 400 dauke da COVID-19.