A yau Juma’a kasar China ta ce adadin mutanen da suka mutu a birnin Wuhan a sanadiyyar annobar COVID-19 ya fi yadda aka zata da farko.
Wuhan, birnin da annobar ta fi kamari a China, ya kara adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar da sama da kashi 50 cikin 100. A wata sanarwa jami’an kiwon lafiyar yankin sun ce karin wasu mutane 1,290 sun mutu sakamakon annobar, abinda ya sa jimlar mace-macen ta kai 3,869.
Sanarwar ta kuma ce akwai dalilan da suka sa aka samu bambanci a adadin, ciki har da yawan marasa lafiyar da suka fi karfin kayan aikin asibiti da cibiyoyin kiwon lafiya, da kuma wasu mutane da suka mutu a gidajensu da ba a sa su cikin lissafin farko ba.
Jami’an kiwon lafiyar kasashen ketare sun sha nuna shakku akan adadin mace-macen da aka samu a kasashen Asiya, suna cewa kididdigar da China ta fitar kadan ce idan aka kwatanta da ta sauran kasashen duniya.
Ya zuwa yanzu dai adadin mutanen da suka kamu da wannan cutar a kasashen duniya ya haura miliyan biyu, kana wadanda suka mutu sun fi 150,000, a cewar cibiyar binciken annoba ta jami’ar Johns Hopkins.