Coronavirus Ta Haifar Da Babban Gibi a Kudaden Da Amurka Ke Samu

Baitul Malin Amurka

Baitul Malin Amurka

An yi kiyasi yawan kudin ya kai dala biliyan 864, adadin da ya haura abin da Amurka ke gani na gibi a duk shekara a tarihin kasar.

Gwamantin Amurka na fuskantar karin wadanda suka kamu da COVID-19 da kuma tasirin da cutar ta yi kan attalin arzikin kasar, lamarin da ya haifar da babban gibi kan kudaden da ake sa ran samu a watan Yuni.

An yi kiyasi yawan kudin ya kai dala biliyan 864 adadin da ya haura abin da kasar take gani na gibi a duk shekara a tarihin kasar.

Gibin ya faru ne yayin da fadar White House da Majalisa suka amince da tiriliyoyin daloli na gagarumin wasu shirye shiryen tallafi don yaki da coronavirus, a yayin da sama da ma’aikata miliyan 40 aka sallama daga bakin aiki, lamarin da ya rage kudaden da kwastomomi ke kashe – ya kuma shafi kudaden harajin da ake karba.

Alkaluman na watan Yuni ya haura gibin da aka gani a watan da ya gabata wanda ya kai dala biliyan 738 a watan Afrilu, yayin da coronavirus ta fara yaduwa a sassan kasar.

Yanzu, kamar yadda takardun kashe kudade na gwamnati ke nuna alamun ana shiga kangi wata bayan wata, kasar na fuskantar karin adadin wadanda suke kamuwa da coronavirus, inda a ‘yan kwanakin nan ake ganin sama da mutum dubu 60,000 suna kamuwa da cutar.