Wasu mazauna kan iyakokin kasashen biyu sun yi kira ga gwamnati da ta dauki matakai kan ‘yan kasuwa da suke zirga zirga tsakanin kasashen.
Sannan sun yi kira ga jama’a duk wanda ya ji alamun wata rashin lafiya da ya garzaya asibiti mafi kusa domin duba lafiyarsa.
Gwamnatin Najeriya dai yanzu ta kara tsaurara matakai na shigowa cikin kasarta, musamman ta filin jiragen sama da ta nan ne wani dan kasar italiya ya shiga, wanda bayan an gwada shi a jihar legas aka gano yana dauke da cutar ta coronavirus.
Kamfanin da mutumin yake aiki a jihar Ogun sun killace wasu mutane 28 da ake kyautata zaton sun yi mu’amala da shi bayan da ya dawo daga wani balaguro.
Ministan Lafiya na Najeriya, Mr. Osagie Ehanire, ya bada sanarwar cewa gwamanti na daukan matakan magance yaduwar cutar coronavirus a kasar da kuma matakan kare bullar cutar a ko da yaushe.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5