A Najeriya, rahotanni daga cibiyar kare kamuwa da cututtuka da ake kira NCDC a takaice, a bayanin da ta gabatar yau Talata da asuba ta ce yawan mutanen da suka harbu da cutar coronavirus mai shafar numfashin bil’adama sun kai 40 a fadin Najeriya.
A dangane da haka ya sa gwamnatocin jihohin Bauchi da kuma Gombe suka himmatu wajen dakile yaduwar cutar a jihohinsu ta hanyar kafa wasu kwamitoci na kwararru, da shugabannin al’umma da kuma na addini domin fadakar da al’ummominsu hanyoyin da zasu kare kansu daga cutar.
A jihar Bauchi, mukaddashin gwamnan jihar Sanata Baba Tela ne ke jagorantar kwamitin da zai tabbatar da gudanar da kemfen fadakarwar akan hanyoyin da jama'a zasu bi don kaucewa kamuwa da cutar ta coronavirus.
Kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Maigoro, ya ce a halin da ake ciki yanzu, ya zama wajibi jama’a su kula da tsaftace muhalli da jikinsu su ta hanyar yawaita wanke hannu, da kuma rage cinkoso.
Babban mai ba gwamnan jihar Bauchi shawara a fannin labarai, kwamared Muktar Gidado ya yi karin haske akan gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammed, da ya killace kansa a sanadiyar shan hannu da ya yi da dan tsohon mataimakin shugaban Najeriya Mohammed Atiku Abubakar wanda aka tabbatar yana dauke da cutar. Kwamared ya tabbatar da cewa a halin yanzu dai babu wasu alamomi dake nuna cewa gwamnan ya kamu da cutar amma duk da haka an dauki jininsa don a je a yi gwaji a Abuja.
Hakazalika gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya kafa wani kwamiti na wayar da kan al’ummar jihar game da hanyoyin da zasu bi don kaucewa kamuwa da cutar coronavirus. Kwamitin mai wakilai 21, wanda farfesa Idris Muhammed ke jagoranta zai tabbatar da cewa an toshe duk wata kafa da zata bada damar shigowa da cutar coronavirus.
Cikin matankan da aka dauka a jihohin sun hada da rufe makarantu da kuma sa ido akan taron mutane.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5