Kungiyar malaman Jami'a ta ASUU a Najeriya ta ce barkewar annobar cutar coronavirus ce ta sa malaman suka dakatar da tattaunawar da suke yi da gwamatin kasar.
A kwanan ne hukumomin Najeriya suka yi barazanar maka malaman jami’ar a kotu muddin ba su koma teburin tattaunawa ba a rikicin da bangarorin da suke yi.
Sai dai daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar, Farfesa Muntaqa Usman ya ce da ma suna tattauna da gwamnati amma zuwan annobar cutar COVID-19 ya sa aka dakatar da tattaunawar.
Ya kuma ce maganar tattaunawar ta danganci bukatun yarjejeniyar da suka sanya wa hannu da gwamnati a shekarar 2009 amma an sabunta ta don tantance ko an yi abubuwan da aka ce za a yi a yarjejeniyar ko akasin haka.
“Ci gaban kasa ya ta’allaka ne akan al’umma mai ilimi kuma jami’o'i suna taka muhimmiyar rawa wajen ilimintar da al’umma. Ya na da kyau a ba fannin ilimi muhimmanci sosai, idan gwamnatin tarayya ba ta dauki matakan bunkasa ilimi ba, ba za a yi maganin matsalolin ba." In ji a Farfesa Muntaqa.
Sannan ya koka kan yadda jami’o’i ke rasa kwararrun malamai saboda yadda takaddama tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya ta ki ci ta ki cinyewa shekara 11 kenan.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5