Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun tabbatar da cewa cutar coronavirus ce ta hallaka ministan kwadagon kasar, kuma shugaban jam’iyar PSD Basira, Mohamed Ben Omar, wanda ya rasu a yammacin ranar lahdi a babban asibitin Hopital General de reference dake birnin Yamai.
Shugaban kasar Issouhou Mahamadou ya jagoranci jana’izar fitacen dan siyasar kafin daga bisani aka wuce da gawarsa zuwa makabartar unguwar Yantala.
Rasuwar ministan kwadago Ben Omar Mohamed wacce ta zowa jama’a da bazata ta matukar girgiza daukacin ‘yan Nijer wadanda a fili suka nuna juyayi akan wannan al’amari, da suke kira da babban rashi, saboda kyawawan halayen fitacen dan siyasa. Abokan aikinsa a gwamnatance irinsu Ministan watsa labarai Salissou Mahamadou Habi yayi wa marigayin kyaukyawar shaida.
Haka su ma mataimakansa a jam’iyar PSD Basira sun yaba da dattakon shugaban na su, saboda a cewar su ba ya gajiya da baiwa makusantansa shawarwari akan zamantakewa.
Hajiya Zeinabou Badje ita ce shugabar matan PSD Basira, ta ce, an samu babban rashi rashi a Jamhuriyyar Niger.
Ministan cikin gida Bazoum Mohamed dake matsayin dan uwa na jini ga Ben omar Mohamed ya tabbatar wa wakilin Muryar Amurka da wayar tarho cewa, marigayin ya yi fama ne da cutar coronavirus kafin rai ya yi halinsa.
A yau litinin ne aka yi jana’izarsa a babbar asibitin Yamai cikin yanayin mutunta matakan dakile yaduwar cutar COVID-19. ya kuma samu gaisuwar ban girma daga shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou da mambobin gwamnati kafin a yi masa rakiya zuwa makarbartar Yantala.
Dan asalin karkarar Goure ta yankin Zinder, minista Ben Omar Mohamed malamin tarihi ne da kimiyar Geographie ya rasu yana da shekaru 55 a duniya sannan ya bar mata daya da ‘ya’ya shida.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5