Hukumomi a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bada umarnin takaita zirga zirga a kasuwannin jihar a kokari na takaita yaduwar cutar Coronavirus.
Ta kuma bada umarnin rufe dukkanin cibiyoyin gudanar da taron bukukuwa a birni da kewayen Kano.
Hakan dai na faruwa yayin da aka shiga rana ta biyu da rufe kanana da manyan makarantu a jihar ta Kano.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi jawabi ga al’ummar jihar dangane da matakan da gwamnati ke dauka na toshe kafofin da cutar Corona ka iya shiga jihar.
“Duk wuraren da ake bukukuwa an rufe su, kuma gwamnati ta jingine duk wani taro,” a cewar gwamnan.
A hannu guda kuma, ita ma gwamnatin jihar Jigawa da ke makwabtaka da Kano ta kafa nata kwamitin fadakar da jama’a game da wannan annoba ta Coronavirus.
Sai dai kokarin samun karin haske daga mahukuntan jihar game da matakan gwamnati akan wannan annoba ya ci tura.
Baya ga iyaka da Jamhuriyar Nijar, dukkanin jihohin arewa maso gabashin Najeriya na ketawa ta jihar Jigawa ne kafin shiga jihar Kano domin harkokin kasuwanci da sauran al’amuran zamantakewa na yau da kullum.
Ga cikakken rahoton a sauti.
Your browser doesn’t support HTML5