Ma’aikatar lafiya a jihar Plateau da ke tsakiyar arewacin Najeriya, ta ce har yanzu ba ta tabbatar ko mutum 43 da ta killace suna dauke da cutar Coronavirus ba.
Kwamishinan lafiya a jihar, Dr. Nimkong Ndam Lar ya ce sun killace wasu ‘yan kasar China da ke aikin hakar ma’adinai a karamar hukumar Wase, tare da wasu ma’aikatan da suka yi cudanya da su.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa, mutum 43 da aka killace, na daga cikin wadanda suka yi cudanya da wasu ‘yan kasar China hudu, wadanda suka dawo daga kasarsu a kwanan nan.
Sun kuma biyo ta Addis Ababa ne, babban birnin Ethiopia a cewar NAN, kamar yadda jaridar The Guardian ta bayyana.
A makon da ya gabata 'yan kasar ta sin suka isa jihar.
Rahotannin sun ce hukumomin jihar sun ce za a ci gaba da killace mutanen har zuwa kwana 14.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa a jihar Pilato, Mr. Dan Manjang ya ce gwamnati ta shirya don dakile duk cututtuka masu yaduwa.
Ya kuma gargadi masu yada labaran karya kan cutar da su guji yin hakan.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji daga Jos, babban birnin jihar Plateau:
Your browser doesn’t support HTML5