Coronavirus: An Fara Sallamar Fasinjojin Dake Tsare a Wani Jirgin Ruwa

Diamond Princess a Yakohoma Japan

Daruruwan fasinjoji sun fara barin jirgin ruwan shakatawar da aka tsare tsawon makwanni biyu a tashar jiragen ruwa ta kasar Japan a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar Coronavirus da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 2,000 a kasar China.

Diamond Princess

Ana sa ran kimanin fasinjoji 500 da suka warware za su bar jirgin ruwan na Diamond Princess ranar Laraba a Yokohama, inda jirgin ya sauka tun lokacin da ya isa garin a ranar 3 ga watan Fabrairu.

Jami'an lafiya na Japan sun kebe fasinjoji 3,700 da ma’aikatan jirgin don sa ido a kansu bayan da aka gano cewa wani fasinja da ya sauka a Hong Kong na dauke da kwayar cutar ta Coronavirus a shekarar 2019.

Amma kokarin shawo kan yaduwar kwayar cutar ya fuskanci koma baya yayin da tuni mutane 542 suka kamu da cutar, lamarin da ya kasance gungun jama’a mafi girma da aka tabbatar sun kamu da cutar a wajen China.