A yayin da a gobe juma’a 1 ga watan Mayu, ta ke ranar bikin ma’aikata ta duniya, kungiyoyin kwadago a Jamhuriyar Nijer sun ba da sanarwar soke dukkan wasu shagulgulan da aka saba gudanarwa a kowace shekara, da nufin mutunta ka’idodin da gwamnatin kasar ta shimfida domin dakile yaduwar cutar coronavirus.
A kan yi jerin gwano da taron gangami da liyafar cin abinci da ma’aikata a kowace ranar 1 ga watan Mayu, yayin da ranar ke zama wani bukin karrama ma’aikatan da suka nuna kwazo akan aiki, tare kuma da gabatar da takardar jerin bukatun ma’aikata ga hukumomi.
To sai dai Mahaman Zaman Allah, babban magatakardan gamayyar kungiyoyin kwadago ta USTN, ya ce, wannan shekarar ba za a sami gudanar da irin wannan bikin ba, saboda anobar cutar coronavirus da ta addabi duniya.
Amma uwar kungiyar ta USTN ta ce, batun yaki da annobar COVID-19, ba zai sa ta sha’afa da maganar neman hakkokin ma’aikata ba.
Shugabannin kungiyar jami’an kiwon lafiya ta SUSAS, wani sash na hadediyar kungiyar kwadago ta CDTN, sun yi rangadin dudduba cibiyoyin bincike da asibitoci daban-daban domin karawa ma’aikata azama, a cewar Sakataren kungiya Ibro kane.
Tuni dai ma’aikatar kwadago ta Niger ta hanyar wata sanarwa mai dauke da sa hannun minista Ben Omar Mohamed, ta bayyana ranar ta 1 ga watan Mayun 2020, a matsayin ranar hutu a fadin kasar, domin tunawa da zanga-zangar da ma’aikatan birnin Chicago su ka gudanar a shekarar 1886 da nufin samun kyakkyawan yanayin rayuwa da na aiki.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5