Coleen Rooney Tana Zargi Ana Fitar Da Bayananta Ga ‘Yan Jarida

Wayne Rooney

Uwargidan dan wasan kwallon ta kwashe ‘yan watanni tana kokarin zakulo wanda ke fitar da bayananta ga ‘yan jarida da kuma dalilin yin hakan.

A wani tarko da ta dana domin gano wanda ke fitar da bayananta na shafin sada zumunta ga manema labarai, Coleen Rooney ta gano daya a cikin matan ‘yan wasan kwallon kafa Rebekah Vardy matar Jamie Vardy dake wasa a Leicester City ce take mata wannan aika-aika.

Uwargidan Rooney mai shekaru 33 da haifuwa wacce ta shahara a shafukan yanar gizo kuma tana da masu bibiyan harkokin sama da mutane dubu dari takwas amma kalilan ne a cikin su ta zaba suna iya ganin bayananta na sirri.

Tace a cikin wadannan mutane kadan da ta yarda dasu, sai daya a cikin su ya fara fitar da wasu bayananta ga jaridar The Sun, saboda ta ga wasu bayanata da ta kafe a shafin sada zumunta a kan jaridar ba tare da saninta ko kuma amincewarta ba.

Rooney da take cike da haushi a kan wanda ke fitar da bayananta ta yanke shawarar yin wata dabarar zakulo mai wannan aiki saboda ta san a cikin masu bibiyanta ne suke wannan aikin kuma da haka ta gano Rebekah Vardy wacce ta dade tana tunanin itace ke aikata wannan danyen aiki take fitar da bayanta na sirii.