Mrs Clinton ta yi Tir da Sakin Bayanan Sirri da Wikileaks ta yi

  • Ibrahim Garba
Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton na jawabi

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton na jawabi

Amurka ta yi tir da fallasa wasu sirrin diflomasiyya kimanin 250,000 da Wikileaks ta yi.

Amurka ta yi tir da fallasa wasu sirrin diflomasiyya kimanin 250,000 da Wikileaks ta yi.

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta ce sakin wadannan bayanan hari ne kan manufofin harkokin wajen Amurka da kuma duniya baki daya. Ta ce Amurka na kan daukar tsauraran matakai don hukunta wadanda su ka sace bayanan, kuma tan a daukar matakan ganin irin wannan keta haddin bai sake faruwa ba.

Mrs Clinton ta ce sakin wadannan bayanan ya jefa rayukan wasu ciki hadari, ya yi barazana ga tsaron kasa tare da kawo cikas ga kokarin Amurka na aikin da wasu kasashe don warware matsaloli bai daya. Mrs Clinto ta ce ta na son a fahimci cewa manufofin harkokin wajen Amurka sam ba shigin irin wadanda aka fallasa din ba ne, kuma manufofin Amurka ba abubuwa ne boyayyu ba.

Wasu labaran cikin kunshin bayanan da aka saki sun nuna cewa Amurka ta bukaci jami’an diflomasiyyarta su samo bayanan sirri game da jami’an Majalisar Dinkin Duniya irinsu lambobin Katin biyan kudi na Credit Kat da makamantansu. An ce wai su kuma samo bayanan halittansu na DNA da hotunan tsakar ido na jami’an harkokin wajen kasashen da wasu batutuwa su ka hada su da Amurka.