Clinton Ta Fara Ziyarar Aiki Na Kwanaki 10 A Afirka

Sakatariyar Harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.

Talatan nan Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta tashi zuwa Senegal, kasa ta farko da zata yada zango a fara ziyarar aiki na kwanaki 10 a nahiyar Afirka.

Talatan nan Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta tashi zuwa Senegal, kasa ta farko da zata yada zango a fara ziyarar aiki na kwanaki 10 a nahiyar Afirka, da zummar bunkasa matakan raya tattalin arziki da demokuradiyya.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce sakatariya Clinton zata gana gobe laraba da sabon shugaban Senegal Macky Sal, kuma zata jinjina wa Senegal a matsayin kasa wacce demokuradiyya ta sami zama da gindinta.

Mr. Sall sabon shugaban na Senegal, shine ya kada tsohon shugaban kasa Abdoulaye Wade a zaben da aka yi cikin watan Maris, bayan da aka samu gardama kan ko shin ya cancanta tun farko ma Mr. Wade ya nemi wa’adi na uku.

Haka kuma ana sa ran madam Clinton zata kai ziyara sabuwar kasa ta Sudan ta kudu,bayan ta balle daga Sudan a cikin shekarar da ta shige.

Ziyarar da zata kai Sudan din, tazo ne a lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yake muhawara kan irin matakai da suka dace ya dauka na kawo karshen rikici kan rabon arzikin mai, batun kan iyaka, da kuma batun zama dan kasa, matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa, tsakanin kasashen biyu.