Hakan yasa majalisar dinkin duniya ta kebe ranar 29 ta kowace watan Satumba a matsayin ranar fadakar da al'umma akn hanyoyin da za'a bi a gujewa kamuwa da ciwon zuciya.
Farfasa Solomon Sule Dan Bauchi likitan cututuka da suka shafi hakarkari da zuciya a asibitin koyaswa na Jami'ar Jos yayi bayani akan yadda ake kamuwa da cutar.
Yace kamar mace dake da juna biyu idan ta samu ciwo yana iya taba yaron cikinta wanda kuma ka iya taba zuciyar yaron. Idan kuma mutum ya manyanta yana iya samun hawan jini. Akwai wasu abubuwan kuma da ka iya kawo ciwon zuciya. Giya na iya kawo ciwon zuciya. Ciwon suga shi ma yana iya kawo ciwon zuciya. Akwai alamomi da yawa. Kasala da rashin karfi na cikin alamomin. Idan mutum na tafiya ba zai tafi da nisa ba sai ya gaji da kuma nunfashi. Wani zubin kuma a cikin barci sai mutum ya ji kamar ya shake domin nunfashi baya tafiya yadda ya kamata.Kafafuwa da fuska na iya kumbura
Dangane da yadda za'a gujewa ciwon zuciya Farfasa yace idan mace nada juna biyu kuma tana zuwa gwaji to za'a gane a yi magani. Wanda ya manyanta ya dinga zuwa ana gwadashi wajen likita. Ya kuma rage cin gishiri. Ya dinga attisahi ko motsa jiki. Ya rage cin maiko. Ya gujewa shan taba. A rage kiba. A rage soye soyen abinci. A dingi cin ganye da 'ya'yan itace.
Ga karin bayani daga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5