Ciwon 'Ya Mace -Mahimmancin Sana'a Ga Mata III

Aisha Mu'azu

A wannan makon ma kamar a makon jiya, mun ci gaba da tattaunawa da malama Fatima Muhammad Uwattara, malamar addini, 'yar kasuwa kuma mai jagorantar makarantar Dangana International School mai zaman kanta a Ghana da hajiya Sa'adatu Ala Kurawa, malamar jinya mai ritaya, mai sasanta tsakani a al'umma sannan mai bada gudunmawa wajen bunkasa rayuwar mata a jihar Kano. Kuma mu mai da hankali ne akan mahimmancin aiki ko sana'a ga mace da kuma batun darajanta sana'a duk kankantar ta, baya ga mahimmancin mace ta fahimci alfanun samun sahalewar mijinta domin yin sana'ar ko aiki.

A latsa nan domin a saurari cikaken shirin:

Your browser doesn’t support HTML5

CYM EP 185 Mahimmancin Sana'a Ga Mace III.mp3