Sakamakon annobar coronavirus da kuma karyewar farashin man fetur a kasuwar duniya ya sa gwamnati ta yi wa kasafin kudin na bana sauyin fasali babu shiri, inda Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa majalisar Naira Triliyan 10 da digo 5, amma kuma majalisar ta kara yawan kasafin zuwa Naira Triliyan 10 da digo 8.
Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya ce rikicin annobar coronavirus ne ya sa aka yi karin na Naira Biliyan 500 a cikin kasafin don a magance yaduwar cutar. Ya kuma ce sun yi la'akari da karin kudin da kuma yadda za a samu damar aiwatar da kasafin.
A cikin hukumomin gwamnati da suka samu kari a kasafin har da Ma'aikatar Kiwon Lafiya a cewar Sanata Ibrahim Shekarau, ya kuma ce gwamnati ba ta da hurumin kashe ko sisi a kudaden da aka tara na gudumuwar tallafin coronavirus, dole sai ta kai batun gaban majalisar dokoki don su bada amincewarsu, saboda haka aka kara yawan kudin ma'aikatar kiwon lafiya.
Wasu basussuka da gwamnatin tarayya ta ci na daga cikin dalilan da suka sa aka yi wa kasafin kwaskwarima. Dan Majalisar Wakilai Sada Soli Jibiya, ya ce dole ne majalisa ta amince da bashin dalar Amurka biliyan 5 da digo 5 domin a samu a yi wa al'umma aiki, ya kuma jaddada cewa babu kasar da ba ta cin bashi a duniya.
Sada ya kara da cewa gwamnatocin baya sun ci bashi kuma na gaba ma za su ci bashi, haka ake aikin gwamnati a duk duniya, wani abu da ya yi wa lakabi da jari hujja.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5