Wasu rahotanni na bayyana cewa shugaban gasar lig na La-Liga ta kasar Spain Javier Tebas, yace za a iya dakatar da cinikin dan wasan da Barcelona tayi daga Atletico Madrid Antoine Griezmann, sakamakon takaddama kan farashin dan wasan da ake yi tsakanin tsohowar kungiyar tasa.
Bayan da Barcelona ta kammala sayen dan wasan a kwanakin baya, sai kungiyar Atletico Madrid ta koka kan farashin da aka sayi Griezmann Yuro miliyan €120 kimanin fam miliyan £107.
Hakan na nuni da cewar farashin dan wasan ya sauko daga Yuro miliyan
€200, zuwa £120 a ranar 1 ga watan Yuli, 2019, inda Atletico tace sunyi yarjejeniyar tun kafin wannan ranar.
Shugaban La-ligar Tebas, ya bayyana cewa gasar ta La-Liga za ta duba kafun ta yanke hukunci kan matakin da za ta dauka na gaba idan aka duba hakane to zai iya yiwuwa a dakatar da sayen dan wasa.