Misali a kwanan nan aka sami wata mata da ta yanke gaban wani dan jariri dan kishiyarta da sunan kishi. Baya ga ire-iren wadannan matsalolin da suka sha faruwa a baya har kkawo yanzu. Wannan ce tasa muika yi duba game da abinda ke haddasa wannan matsala.
Wakilinmu na Abuja Hassan Maina Kaina ne ya hada mana rahoton, inda ya tattauna da masana tarihin zamantakewa da al’adun ‘yan Najeriya musamman ma na arewaci. Inda Shehin Malami a Jami’ar Jihar Kaduna Farfesa Ibrahim Malumfashi ya yi tsokaci akai.
Inda ya nuna cewa, bisa ga binciken da aka yi, da ya nuna yadda ake samun karuwar matsalar abubuwan maye ko buguwar da ake samu a tsakanin gidajen matan aure, Farfesan yace, zai fi ta’allaka wannan laifi da shaye-shaye, fiye da yadda ake ta zato ko kishi ne ya ke haddasa faruwar haka.
Bayan wannan kuma, shin wane mataki kungiyoyi masu zaman kansu game da kare hakkin yara ke dauka akan lamarin? Halima Baba-Ahmed ta yi karin haske da cewa suna nan suna sa ido tare da neman yiwa tufkar hanci.
Su ma Lauyoyi irin su Barista Babakura ya bayyanawa Hassan din cewa, wannan babban laifi ne aika-aikar da ake hukunci a bisa doka. Ya kara da cewa, ya ma kamata ne a yiwa dokar kwaskwarimar da zata kara mata karfi da tsanani ga duk wanda ya aikata irin wannan laifi.
Your browser doesn’t support HTML5