Shahararren lauyan nan dan Najeriya da ke Amurka, Malam Aminu Gamawa, ya bayyana matukar goyon bayansa ga yadda Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kokarin hada hancin hukumomin yaki da almundahana, ya na mai kiran da a inganta yanayin hukumomin.
A wata hirar da ya yi ta waya da abokin aikinmu Usman Kabara jiya ta waya, Gamawa ya ce an zabi Shugaba Muhammadu Buhari ne saboda alkawarin da ya yi cewa zai yaki cin hanci da rashawa musamman ganin tarihinsa na mai kyamar rashin gaskiya. Hasalima, in ji shi, Buhari ya shimfida matakan da su ka nuna cewa lallai wannan karan ma ya daura damarar yaki da cin hanci da rashawa. Akwai hukumomi masu yawa da ke yaki da cin hanci da rashawa, ta yadda har wani sa’inma akan samu rudami dangane da wadda za ta bi diddigin wata batakala – a ce ko EFCC ce, ko a ce ICPC, ko Police, ko hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta NDLEA, da dai sauransu. Ya ce saboda wannan rudamin, a maimakon yaki da cin hanci ya kankama sai shi kansa ya shiga fama da matsalar cin hanci. Sau da yawa za ka ga am kama mai laifi, maimakon a gurfanar da shi a kotu a yi abin da ya kamata, sai a shiriritar da abin. Sannan kuma, sai ka ga idan mai laifi na dasawa da jam’iyyar da ke mulki, sai ka ga an yi rufa-rufa.
Gamawa ya ce mafita shi ne a sake fasalin tsarin daukar ma’aikatan hukumomin yaki da almundahana ta yadda za a rika daukar wadanda su ka dace; a kuma rika biyansu yadda ya kamata don kar su jarabtu. Haka zalika, ya kamata a rika nada alkalan kwarai kuma masu gaskiya da rikon amana.
Duk wadannan, a cewar Gamawa, abubuwa ne da za a iya yi a Najeriya tun da an yi su a wasu kasashen duniya.
Your browser doesn’t support HTML5