Cin Hanci Ya Sa Gwamnatin Ghana Rusa Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasar

'Yan wasan kwallon kafa na Ghana

Binciken sirri da wani dan jarida Anas Arniya Anas ya gudanar ya bankado yadda jami'an hukumar kwallon kafa ta Ghana da alkalan wasa ke karban cin hanci tare da shirya sakamakon wasa kafin ma a yi wasan.

Al'umma kasar Ghana sun samu ganin bidiyon da ya bankado wata badakalar cin hanci da rashawa da munamuna a hukumar kwallon kafa ta kasar inda suka ga jami'an hukumar da alkalan wasanni suke karban na goro.

Wani fittacen dan jarida da aka sani da badda kama wurin yin bincike, Anas Arniya Anas shi ya gudanar da binciken sirrin akan munamunan da hukumar kwallon kafar Ghana ta dade tana yi.

Abubuwan da bidiyon ya nuna ya girgiza al'ummar Ghana saboda sun ga yadda jami'an hukumar da alkalan wasa ke watanda da kudaden da suka tara ta sayar da wasanni da aiwatar da rashin gaskiya.

Ganin irin kazantar da ta faru a hukumar, gwamnatin kasar ta dauki matakan rushe hukumar kamar yadda ministan ma'aikatar matasa da wasanni Mr. Shiyaba ya sanar.

Wani mai fashin baki Malam Isa Jibrin Mai Rago ya yaba da aikin binciken da dan jaridan ya yi ya kuma ce abun da suka gani ya girgizasu da ma al'ummar Afirka saboda irin cuwa-cuwan da suka gani ana aiwatarwa har da shirya sakamakon wasa kafin ma a yishi.

A saurari rahoton Ribwan Abbas da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Cin Hanci Ya Sa Gwamnatin Ghana Rusa Hukumar Kwallon Kafar Kasar - 3' 06"