A halin da ake ciki, masu tallace tallace ko daukar nauyin wasanni na hukumar FIFA sun yi kira ga hukumar da ta yi wasu canje canje, a yayin da shugabannin hukumomin kwallon kafa na nahiyoyi da yankunan duniya suke muhawara a kan makomar shugaban FIFA dake fuskantar suka.
Wannan yana faruwa ne a bayan da kasashe nAmurka da Switzerland suka kaddamar da babban bincike kan cin hanci da rashawa a cikin hukumar ta FIFA.
Kamfanin Katin Bashi na Visa ya bada sanarwa mafi karfi inda ya bayyana matukar takaicin kama wasu jami’an hukumar FIFA da aka yi bisa zarge-zargen zarmiya da cin hanci, yana mai cewa zai sake nazarin daukar nauyin wasannin hukumar idan har ba a gudanar da sauye-sauye ba.
Shima kamfanin lemo na koka kola ya nuna damuwar sa kan zargin da ake yiwa hukumar kwallon, yana kuma sa ran hukumar zata yi bayani kan maganar, ya in da kamfanin Adidas yayi kira ga hukumar da ta bi duk sharuddan da aka gindaya na kungiyar a fili.
A halin da ake ciki kuma hukumar kwallon kafar Asiya ta fada yau Alhamis cewa a cigaba da zaben da aka shirya gudanarwa gobe Juma’a na neman sabon shugaban kungiyar, tana kuma goyon bayan mai neman takara kuma shugaban hukumar na yanzu Sepp Blatter.