A yau Talata ne Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta bada adadin mutanen da aka kashe a Yemen cikin watanni 18 zuwa dubu goma, a yayind da fadar ke ci gaba da jefa miliyoyin yan Yemen cikin tsananin bukatar taimakon agajin gaggawa
WASHINGTON DC —
Shugabar sashin bada agaji na MDD Jamie McGoldrick tace tana yiwuwa wa’yannan akaluman su fi abin da aka bayyanar.
Kafin yau Talata, jami’an MDD suna fadin akalla mutane dubu shida ne suka mutu a wannan yakin kungiyar ‘yan tawayen Houthi dake samun goyon bayan Iran. ‘Yan tawayen suna adawa ne da gwamnatin shugaba Abdu Rabu Mansour Hadi ne.
Bugu da kari akan wannan yakin basasa da ake kai hare-haren sama karkashin jagorancin Saudiya bai taimakawa gwamnati ba, saboda Yemen tana fama da hare-haren yan bindiga ciki har da wanda ya faru a ranar Litinin a Birnin, a tashar jirgin ruwa ta Aden dake kudancin kasar.