Filin Ciki Da Gaskiya na wannan makon ya ci gaba da duba batun korafin jama'a a Kanon dabo, kan yunkurin gwamnatin jihar na raba wasu filaye ko wurare masu muhimmanci ga daidaikun mutane da wasu ke ganin hakan bai dace ba ko ya sabawa doka.
WASHINGTON DC —
Daya daga cikin wuraren da ake zargin gwamnatin jihar Kano da cefanarwa shine filin gidan zakka da ke Goron Dutse cikin badala a tsohon birnin Kano.
Cikin shirin na wannan makon za a aji tsokacin masanin kimiyyar siyasa Dr. Sa'idu Ahmed Dukawa na jami'ar Bayero, wanda ya yi bincike sosai tare da yin rubutu kan filin gidan Zakkah da ake takaddama akai.
A yi sauraro lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5