Ciki Da Gaskiya: Malami Ya Yaudari Marainiya Mai Shekaru 13 Ya Yi Mata Ciki, Afrilu 17, 2023

Sarfilu Hashiim Gumel

Shirin ya sauka a unguwar WATER BOARD da ke Jalingo babban birnin jihar Taraba, inda wata yarinya mai shekaru 13 kacal a duniya mai suna Zainab ta ce malamin ta na allo mai suna Hussaini Mai Guduma Wukari, ya yaudare ta ya yi ta fasikanci da ita, ba tare da a lokacin ta san me zai biyo baya ba, inda a yanzu ta ke da ciki da ya kai wata tara haihuwa yau ko gobe.

Maganar ta isa Majalisar malaman musulunci ta Taraba, ofishin ‘yan sanda har ma ta kai ga kotu da wasu kungiyoyin kare hakkin mata.

To sai dai da shirin ciki da gaskiya ya tuntubi Mallam Mai Guduma, ya ce sam sharrin makiya ne kawai, amma ba shine da alhakain cikin na Zainab ba.

Ayi sauraro lafiya:

Your browser doesn’t support HTML5

Ciki Da Gaskiya: Malami Ya Yaudari Marainiya Mai Shekaru 13 Ya Yi Mata Ciki - 11'17"

Your browser doesn’t support HTML5

Ciki Da Gaskiya: Malami Ya Yaudari Marainiya Mai Shekaru 13 Ya Yi Mata Ciki - 10'33"