'Yan damfarar da suka so cutar wakilin Muryar Amurka a Katsina, Zaharadeen Sani, sun yi amfani da lambobi da kuma sunaye na karya, amma filin Ciki da Gaskiya ya samu gano sunayen da aka yi amfani da su wajen yin rajistar wadannan layuka.
Da farko akwai wanda yace shine Injiniya Ibrahim Aliyu Minna, wanda ya fara kiran Zaharadeen domin kwadaita masa wannan harkar da suka so yin amfani da ita don sace masa kudi. Yayi amfani da wannan lamba: 09092222652. An yi rajistar wannan layi a Abuja, amma ba a rubuta cikakken suna ba, abinda kawai aka sanya a jiki shine harafin "M."
Wanda aka ce shi ne babban "consultant" da aka bada sunansa a zaman Dr. James Ombode kuwa, lambar da yayi amfani da ita, ita ce 08066459704. An yi rajistar wannan lamba da sunan "AGAMA" wanda suna ne da 'yan kabilar Eggon a Jihar Nassarawa suke amfani da shi. Akwai wani dan damfara da yayi suna a Jos, Jihar Filato, mai irin wannan suna, amma babu tabbas ko shine wannan.
Sannan akwai wanda aka ce shine dillalin kaya a Katsina mai suna Malam Musa, wanda yayi amfani da wannan lamba: 08062755609. An yi rajistar wannan lamba ce da sunan "OKORI" wanda suna ne na 'yan wata kabila a yankin Niger Delta.
'Yan damfarar sun nemi Zaharadeen ya saka kudi cikin wani asusu ko "account" mai lamba 0073345290 mai dauke da sunan Nura M. Abubakar a bankin Diamond Bank.
Tuni dai Ciki da Gaskiya ya mika wadannan bayanai ga hukumomin da ya kamata su sani a Najeriya.