Washington DC —
Biyar daga ma’aikatan da a ka kafa cibiyar gyaran dabi’a ta nakasassu a birnin Abuja, da ke koyar da sana’o’i sun tunkari shiri nan, su ka ce an kore su daga aiki ba bisa ka’ida ba da kuma hana su albashin watanni da dama.
Ma’aikatan sun ce ba kawai korafin su kora ko rashin samun albashi ba ne, a’a sun a zargin shugaban cibiyar da cin zarafin wadanda a ka ajiye a cibiyar, keta haddin mata da ma matakan da su ka kai ga mutuwar wasu daga wadanda a ke gyarawa dabi’ar.
Zargin da shugaban cibiyar ya musanta tare da bayyanawa shirin abin da ya faru.
Saurari shirin kashi na biyu:
Your browser doesn’t support HTML5