Cibiyar ARDP Ta Ce Yan Najeriya Su Tashi Su Kare Kansu

Sojojin Najeriya a wata gwabzawa da Boko Haram

A cigaba da kiraye kirayen da kungiyoyi da daidaikun 'yan Najeriya ke yi na a kara kaimi a matakan da ake daukawa na kawo karshen tabarbarewar tsaro a Najeriya, wata kungiya ta ce lokaci ma ya yi da za a shiga kare kai.

Cibiyar bincike da bunkasa Arewacin Najeriya (wato ARDP a takaice), ta gudanar da wani taro a Kaduna don tattaunawa akan batun shawo kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya.

Cibiyar ta shirya wannan taron ne domin yin dubi akan matakan da ya kamata a dauka domin magance tabarbarewar tsaro da ke addabar wasu garuruwan arewacin Najierya.

Shugaban Cibiyar ta ARDP, Dr. Usman Bugaje, ya ce lokaci ya yi da za a ba al’umma dama su kare kawunansu.

Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya ta INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya ce sha’anin tsaro a jahohin arewancin Najeriya dole ne sai an hada karfi da karfe domin a shawo kan lamarin. Ya yi kira ga gwamnati, da jami’an tsaro da sarakuna da matasan kasar su hada hannun domin magance matsalar tsaro a Najeriya, dole kowa ya bada gudunmuwa a fito da bayanai a yi nazari domin samun hanyoyin da za a dakile ta’addanci a kasar.

Shima Dr. Umar Tanko Yakasai, ya nuna damuwarsa game da rashin halartar jami'an gwamnati wajen taron, kuma ya yi kira ga gwamnati da ta dauki harkar tsaro da mahimmanci.

Saurari Rahoton Isah Lawal Ikara Cikin Sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Cibiyar ARDP Ta Gargadi Yan Najeriya Da Su Tashi Su Kare Kawunansu