Salman Khan zai sake kwana a kurkukun Jodhpur, saboda kotun Jodhpur, jinkirta karar sa da ake saurare, biyo bayan belin sa da lauyan taurararon dan wasan ya nema.
An yanke wa tauraraon dan wasan ne hukuncin daurin shekaru 5 a gidan kaso, bayan samun sa da laifin kashe wasu nau’in bareyi guda biyu a shekarar 1998.
Salman Khan, dai ya kwana a kurkukun Jodhpur. Jiya Alhamis lauyan sa HM Saraswat, ya saka takadar neman belin sa bayan da kotu ta saurarai tuhumar da ake masa inda ta yanke masa daurin shekaru 5 a gidan yari, Sarswat ya bayana cewa za a saka takardar tuhumar da ake masa nan ba dadewa ba.
Kamfanin fina-finai na Bollywood dai ya damu da wannan lamari, inda ya ce idan Salman Khan bai samu beli ba hakan zai zama babbar asara ga kamfanin a cewar wani mai fashin baki dake kuma kasuwancin fina finan India, Komal Nahta babu tauraron ‘yan wasan fina finan india da zai iya bada tabbacin gagarumar nasarar a kamfanin ke sa rai.
Your browser doesn’t support HTML5