Firimiya Likeqiang ya fadawa wakilan China na bukatar fadada tattalin arzikinta da kaso 6.5 na ma’aunin arzikin kasa a shekarar da muke ciki ta 2017.
Firimiyan yayi alkawarin tunkarar daya daga cikin matsalolin kasar da ake gani a zahiri na gurbatacciyar iska . yace gwamnati zata kara azama wajen kokarin kula da gurbatacciyar iska ta hanyar cire tsofaffin ababan hawa daga kan hanya da kuma kara karfin gwiwa wajen amfani da Motocin da basu gurbata iska.
Li yace kowa na da hakki wajen samun nasaraakan wannan matsala, “ Indai har al’ummar mu zata cigaba da kokari, to zamu cigaba da ganin sararin samaniya tarwai a kowacce shekara da zatazo.
Ya kara da cewa China zata kara matasawa gaba wajen karewa da kuma tsare gurbatar Ruwa da kasa.
A kasar China ta samu Karin kaso 6.5 zuwa 7 cikin dari wanda yak are a kaso 6.7 cikin dari, wanda ya kasance marar sauri a cikin shekaru 26 da suka gabata.
Shuwagabanni a China sunyi haluri da Jan jikin Karuwar tattalin arzikin domin samar damar kula da yawan basussuka.