China Zata Taimaka Nemo Daliban Cibok

Firimiya Li Keqiang

Firayim ministan Chana Li Keqiang ya gana da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ana dab da fara Taron Tattalin Arzikin Duniya a Abuja Larabannan.
Shugaban Najeriya yace Li ya mika hannu yana tayin bada agaji wajen ceto dalibai mata sama da 200 da aka sace makonni uku, daga makarantarsu ta Sakandare dake Cibok.

Firayim ministan Chanan dai ana kyautata zaton zai tattauna batun tsaro ne a Najeriya, da kuma hadin gwiwa na tattalin arziki tsakanin kasashen guda biyu.

Wannan shine karo na farko da Li yake ziyartar Afirka tun bayan hawansa karagar mulki, kuma bayan ziyarar Shugaba Xi Jinping a watan Maris ta 2013, a lokacin da ya sabonta baiwa Afirka bashin dala biliyan 20 tsakanin 2013 zuwa 2015.