Yau Alhamis Ministan harkokin wajen China, Wang Yi yayi wannan furuci wajen wani taron dan jarida a birnin Beijing. Ya ce ya kamata kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya maida martini ya dauki dukkan matakan da suka kamata na tikarar wannan rikici.
To amma Mr Wang ya kuma jaddada cewa tilas takunkumi da matsin lamba su tafi kafada da kafada da yin shawarwari da Korea ta arewa.
A yayin da China ke cewa tana goyon bayan matakan da Majalisar Dinkin Duniya zata dauka akan Korea ta arewa, ita kuma kasar Rasha tana ta kokarin ganin an amince da Korea ta arewa a zaman kasa mai karfin makaman nukiliya. Kuma Rashan bata goyi ko kuma bata goyon bayan matsayin Amirka da kawayenta akan kasar Korea ta arewa.
A yayin da yake ganawa da shugaban Korea ta kudu Moon Jae’in a Vladivostok yau Alhamis, shugaban Rasha Vladimir Putin ya kara yin kiran da’ayi shawarwari da Korea ta arewa domin magance rikicin nukiliyan.