A yau Asabar, China ta sanar cewa ta takaita safarar shigar da man fetur zuwa cikin Korea ta Arewa, a wani mataki na bin umurnin kwamaitin sulhu Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya saka mata karin takunkumi kan shirinta na gina makamin nukiliya.
A wata sanarwa da ma’aikatar hadahadar kasuwancin kasar ta Sin ta wallafa a shafinta na yanar gizo, kasar ta Sin ta ce za a rika shigar da tacaccen gangan man fetur miliyan biyu ne cikin kacal a shekara, kuma wannan sabon tsari zai fara aiki ne ranar daya ga watan Oktoba.
Amma ma’aikatar ta ce ta dakatar da safarar tsurar man gas nan take.
Shi dai kwamitin sulhun na Majalisar Dinkin duniya ya haramta yin amfani da man fetur da sauran dangoginsa wajen shirin hada makamin nukiliyan na Korea ta arewa, a cewar sanarwar.
A can baya, kasar ta China ta kan goyi bayan Korea ta arewa kan wasu al’amura, amma a kullum ta na kara nuna rashin gamsuwarta kan yadda gwamnatin Kim Jong Un ke tafiyar da kasar.