Kasar China ta mai da martani nan da nan kan sanarwar Shugaba Donald Trump ta shirin saka harajin dala biliyan 60 kan kayan da kasar China ke shigo da su Amurka, tare da gargadin cewa matakin da Amurka ke shirin daukawa zai jefa huldar cinakayya cikin hadari.
A wata sanarwa ta yau dinnan Jumma’a, ‘yan sa’o’i bayan da Trump ya rattaba hannu kan takardar umurnin saka haraji kan kayaki wajen 1,300 da kasar China ke shigo da su Amurka, Ma’aikatar Cinakayyar China ta yi kira ga kasar Amurka da ta yi tunani sosai kafin ta dau mataki nag aba, ta na mai kiran Amurka da ta ja baya daga abin da ta kira ‘bakin rami.’
Ma’aikatar ta kuma bayar da sanarwa a wata takarda ta daban a yau dinnan Jumma’a cewa ta na kan shirin tsara matakan ramuwar gayya saboda harajin da Trump ya bayar da sanarwar sakawa kan karafa da dalma a farkon wannan watan. Ta ce idan ta kama, za ta saka harajin kan kayakin Amurka wajen 128 da ta ke shigo da su cikin China.
Matakin zai hada da yiwuwar saka haraji da kashi 15% kan kayakin Amurka irinsu kayan marmari da nau’ukan gyada da ruwan laimu da ruwan inabi da bututan karfe; sai kuma harajin kashi 25% kan naman alade da kayan dalma.