Yanzu ya tabbata cewar mutane za su iya karbar takardun su na shiga cikin jirgi ba tare da sun yi mu’amala da mutane ba.
Abin da ake bukata shi ne, su nuna ma na’ura mai kwakwalwa kwamfuta fuskokinsu.
A duk lokacin da mutun ya sayi tikitinsa don tafiya daga wata tashar jirgi zuwa wata, abin da kawai yake bukata shi ne, ya saka bayanansa, da kuma ya isa tashar jirgi sai kawai ya kalli wata kyamara, ita kuma kwamfuta ta san shi za ta bashi damar ya wuce ba tare da ya ba da takardunsa na fasfo ga kowa ba.
Tashar jirgin kasar China a birnin Hongpiao, ta kaddamar da wannan na’urar a karon farko, tana mai fatar sauran kasashen duniya za su bi sahu wajen ganin an daina amfani da mutane yayin da mutane ke kokarin shigar da bayanansu a tashoshin jiragen sama.
Wannan tsarin dai zai taimaka wajen ganin an rage cinkoso a tashoshin jiragen sama, a cewar shugaban tashar jirgin Zhang Zheng, wannan shi ne karo na farko da aka fara amfani da wannan na’urar a kasar China, kuma suna farin cikin ganin nasarar tafiyar.
Kamfanin jiragen sama na Spring ya sanar da cewar kimanin mutane 5,017 sun yi amfani da na’urar ba tare da wata matsala ba.
Hakan na nuni da cewar tsarin zai taimaka matuka wajen ganin an magance matsaloli da dama a duk tashar da ake amfani da shi.