China Ta Goyi Bayan a Gudanar Da Bincike Kan Asalin Cutar COVID-19

China ta goyi bayan wata hukuma mai zaman kanta ta gudanar da bincike kan asalin cutar coronavirus.

Amma binciken kai waken ne bayan an shawo kan annobar, a cewar Shugaban Chinar Xi Jinping a jiya Litinin.

Da yake jawabi a wani taron da aka yi ta kafar bidiyo, na babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kan batutuwan lafiya, zauren da ke tafi da harkokin Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), Xi ya ce China na goyon bayan abin da ya kira,”cikakken bin diddigi” game da yadda duniya ta tunkari wannan annobar, amma sai bayan an samu shawo kanta.

Ana kyautata zaton wani daftarin kudurin Kungiyar Tarayyar Turai, wanda ke kiran da a gudanar da bincike kan tushen cutar ta corona da kuma irin matan da aka dauka, zai samu amincewa a wannan satin.

Kasar Australia ta kasance kan gaba a jerin kasashen da ke adawa da irin wannan kudurin binciken, kuma jiya Ministar Harkokin Wajen kasar Marise Payne ta ce kasar ta na son a gudanar da binciken cikin abin da ta kira “adalci, dalla-dalla kuma ba tare da shisshigi ba.”