China Ta Gargadi Shugabannin Masu Zanga Zanga a Hong Kong

Makonni da dama da aka yi ana gudanarda wannan zanga-zangar kan tituna, sun jefa cibiyar hada-hadan kudade ta Asiya cikin mummunan rikicin siyasa.

China ta yi gargadi mai tsauri ga masu neman canji wadanda suka janyo harkoki a Hong Kong suka tsaya cik, bayan sama da watanni biyu da suka yi suna gudanar da zanga-zanga mai zafi.

Yang Guang, kakakin Hukumar kula da harkokin Hong Kong da Macao, ya fadawa manema labarai yayin wani taron tattaunawa a Beijing a yau Talata cewa "lokaci dan kalila ya rage" kafin shugabannin masu zanga-zangar su fuskanci hukunci."

Makonni da dama da aka yi ana gudanar da wannan zanga-zangar kan tituna, sun jefa cibiyar hadahadar kudade ta Asiya cikin mummunan rikicin siyasa, wanda ba’a ga irinsa ba tun lokacin da Birtaniya ta mika mulki ga kasar Sin a shekarar 1997.

Zanga-zangar dai an fara ta ne a watan Yuni bayan da mazauna garin suka fusata da kudirin dokar mika mutane masu aikata laifuka ga China don su fuskanci hukunci.

A sanadin wannan tashin hankalin aka dakatar da dokar, amma zanga-zangar ta ci gaba kuma tuni ta juye zuwa kira ga neman a canja fasalin mulki na yankin.