China Ta Gargadi Amurka Cewa Duk Wata Yarjejeniyar Kasuwanci Da Suka Cimma Babu Sake

Shugaban Amurka Trump da Shugaban China Xi Jingpin

Yin la'akari da yadda shugaban Amurka Donald Trump yake yawan janye kasarsa daga yarjeniyoyi ya sa kasar China ta yi kashedin cewa duk wata yarjejeniyar kasuwanci da China da Amurka suka cimma babu sake

Ita kuwa kasar China gargadi ta yiwa Amurka cewa ta kwana da sanin duk wata yarjejeniyar kasuwancin da suka cimmawa tsakanin su to bafa wani sake, muddin ma shugaba Trump yaci gaba da aiwatar da barazanar sa ta kara kudin fito da wasu sauran matakai game da wannan matsaya da aka cimmawa na kasuwanci.

Wannan gargadin na zuwa ne bayan da sakataren cinikayya na Amurka Wilbur Ross shida mukaddashin Prime Ministan China Liu suka kammala wani sabon zagayen tattaunawa a jiya lahadi a Beijing, da zummar samun daidaito akan harkan kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

A wannan tattaunawar dai ne Beijing tayi ta bayyana kudirin ta na kara sayen kayayyakin Amurka domin rage raran kasuwancin dake tsakanin ta da Amurka.

Yanzu haka dai raran kasuwancin dake tsakanin kasashen biyu yakai na dala biliyan 375 a cikin shekarar data gabata.

Sai dai har aka kammala wannan tattaunawar ba a fitar da sanarwan bayan taro na bai daya ba, haka kumababu bangaren daya bada cikakken bayanin yadda tattaunawar ta kasance.