Yayinda Amurka ta kara yawan haraji na dala biliyan 200 akan kayayyakin da China ke shigowa dasu Amurka, ita ma China ta kara haraji akan wasu kayayyaki da Amurka ke kaiwa kasar ta.
Amma ba ta yi fito na fito da Amurka ba. A maimakon haka, kasar China sai ta nuna karfin ta a wasu hanyoyin.
A cikin wani mataki na ba zata, China ta rage yawan aladun da take kaiwa Amurka har na kimanin dala biliyan 6.5, matakin da zai yi tasiri sosai akan masu kiwon aladu na Amurka, tunda China ita ce kasa ta biyu da ta fi kai naman alade Amurka.
Daukar wannan matakin ya bada mamaki a daidai lokacin da masu kiwon aladun China suke fama da masassarar aladu a garakan su da ake kira “African Swine Fever” da turanci. Wasu rahotanni sun ce makiyayan alade na kasar China suna cikin hatsarin rasa kashi daya cikin uku na dabbobinsu.