A China, majalisar dokokin kasar ta amince da wata doka wacce ta maida shilaifi da zai kai ga daurin shekaru 3 a fursina, ga duk wani dan kasar da aka samu da laifin 'wulakanta ko rashin mutunta taken kasar.
Babban kwamitin majalisar gudanarwa ta kasar ta ayyana gyra ga kundin laiffuka a zai hada da hukunci ga duk wadda aka samu "da gaske" yana wulakanta taken kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Xinhua, ya kuma bada rahoton cewa, kin mutunta taken kasar yana kuma iya janyo 'yan kasar su rasa 'yancin gudanar da harkokin siyasa.
Mataki na bay bayan nan ya zo ne bayan da kasar ta tsaurara inda aka amince mutane su yi amfani da taken kasar. A cikin watan Satumba, kasar ta zartas da doka wacce zata hukunta mutane da dauri na kwanaki 15 idan suka yi amfani da taken kasar a wajen wata liyafa ko walima.