Batun kwarmata bayanan sirrin Amurka da wani tsohon ma'aikacin kwantaragi mai suna Edward Snowden ya yi ya dau wani sabon salo, bayan da aka ce Rasha da China sun leka cikin kudin bayanan sirrin da Snowden ya sacen
WASHINGTON, DC —
Wata fitacciyar jaridar Burtaniya ta ce Rasha da China sun leka cikin wasu manyan kundin sirri, wadanda tsohon ma'aikacin kwantaragin hukumar leken asirin Amurka Edward Snowden ya sace, wanda hakan ya tilasta Burtaniya janye ma'aikatan leken asirinta daga abin da ta kira makiyan kasashen.
Jaridar Sunday Times ta ce an ba da umurnin janye ma'aikatan leken asirin ne, bayan da Rasha ta samu lekawa cikin kudin bayanan sirri har sama da miliyan guda, wadanda ke wajen Snowden yayin da ya bar Amurka a 2013.