Yara takwas sun mutu a wani hari da aka kaiwa wata makarantar firamare a tsakiyar China jiya Litinin.
Wasu daliban biyu kuma sun raunata sakamakon harin a kauyen Chaoyangpo da ke lardin Hubei, in ji sanarwar da ‘yan sanda suka fitar a garin Enshi.
An kama wani mutum mai shekaru 40 da haihuwa kuma ana ganinsa a matsayin babban wanda ake zargin sa a lamarin.
‘Yan sanda ba su bayyana yadda aka kai harin ba, amma da yawa daga cikin yaran makaranta a kasar China, ko dai sun mutu ko sun raunata, sakamakon kisan gilla da wuka a ‘yan shekarun kwanan nan.
An kashe ɗalibai tara a cikin watan Afrilun na shekara 2018 a kusa da makarantar sakandare a lardin arewa maso yammacin Shaanxi, yayin da yara 14 suka ji rauni a wani harin wuka da aka kaiwa ɗaliban makarantar kindergarten a yammacin Chongqing a watan Oktoban bara.