Bisa tsari da al'ada ta hukumar wasannin Firimiya lig ta Kasar Ingila a duk karshen kakar wasa na kowace shekara ana ba duka kungiyoyi ashirin da suka samu fafatawa a gasar, wani Kaso daga cikin kudin da ta ware, inda ake bada mafi tsoka ga kungiyar da ta samu nasarar lashe gasar.
A bana dai hukumar ta ware fam Biliyan £2.4bn domin rabawa wa kungiyoyin, kuma Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ita zata karbi Kaso mafi tsoka har na fam miliyan dari da hamsin da dubu dari takwas, a matsayin wace ta lashe gasar Firimiyar Ingila ta bana 2016/17.
Kason na bana ya samu kari fiye da na bara wanda aka raba fam biliyan £1.6, inda kungiyar Leicester City tafi daukan Kaso mafi yawa sakamakon lashe gasar a shekarar 2015/16.
Bayan haka Gobe za'a buga wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai UCL na shekarar 2016/17, za'a buga wasanne a filin wasa na Mellinium Stadium of Cardiff, dake kasar Wales, mai daukan mutane Dubu Saba'in da hudu da dari biyar, za'ayi wasan da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya, Nijar, kamaru da kasar Chadi.
Saurari karin bayani a nan.
Your browser doesn’t support HTML5