Wasu rahotanni daga kasar Brazil na bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar ta ce dan wasan Brazil din Willian, ba zai samu damar fafatawa a wasan karshe na gasar cin kofin kudancin Amurka da za a yi ranar Lahadi mai zuwa ba sakamakon jinya da zai yi.
Willian mai shekaru 30 da haihuwa wanda yake taka ledarsa a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ya shiga filin wasa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci a wasan da Brazil ta lallasa Argentina da ci 2-0 a wasan kusa dana karshe Semi final a gasar ta Copa America.
Bayan shigansa dan wasan ya nuna yana jin radadi a kafarsa inda hakan yasa aka garzaya da shi asibiti, domin duba lafiyarsa kan lamarin inda aka gano cewa ya samu matsalar cirar tsoka a bayan cinyarsa.
Hukumar tace don haka Willian yana bukatar murmurewa, hakan ya sa ba zai buga wasan karshe da Brazil zata fafata da kasar Peru ba.
Brazil ta lashe kofin kudancin Amurka har sau 8, bayan haka kuma ta samu
nasarar zuwa wasan karshe na gasar karo na 20, kenan a karon farko tun da ta lashe kofin a shekarar 2007 da ta samu nasara daci 3-0 akan kasar Argentina.